Kamfanin OpenAI ya faɗaɗa tsarin tallan ChatGPT Ads zuwa Najeriya da Afirka ta Kudu, inda 'yan kasuwa za su iya tallata hajojinsu ga masu amfani da ChatGPT yayin da suke neman shawarwari kan kayayyaki ko ayyukan da suke buƙata.
A cewar bayanan farashin da aka bayyana, mafi ƙarancin kuɗin talla shi ne dala $25 a rana. Idan aka gudanar da tallan na tsawon kwanaki 30, kuɗin zai kai dala $750, wanda zai iya haura naira miliyan 1, gwargwadon canjin kuɗi da sauran caji.
'Yan kasuwa za su iya amfani da tsarin OpenAI Ads Manager wajen tsara tallansu, zaɓar kasuwar da suke son kaiwa da kuma saita kasafin kuɗinsu da tsawon lokacin tallan.
OpenAI ta bayyana cewa za a ware tallace-tallacen da alamar talla domin kada a rikita su da amsoshin ChatGPT. Kamfanin ya kuma ce masu talla ba za su samu damar ganin sirrin tattaunawar masu amfani ba, kuma tallace-tallacen ba za su rinjayi amsoshin AI ba.
Wannan sabon tsarin na iya samar wa 'yan kasuwar Najeriya wata hanya ta isa ga abokan ciniki yayin da suke tunanin abin da za su saya. Sai dai tambayar ita ce: Shin za ka iya kashe kusan naira miliyan 1 a wata domin tallata kasuwancinka a ChatGPT, ko kuwa za ka fi son Instagram da Google Ads?
Kamfanin Vatar, wanda ya ƙirƙiri wasan intanet na Lagos Life, na tattaunawa da masu zuba jari domin samun sabon jari na dala miliyan 2.5, bayan wasan ya samu masu amfani sama da miliyan 10.
A farkon ƙaddamar da wasan, kamfanin ya samu jarin dala 500,000, wanda ya kai darajarsa dala miliyan 10.
Daga cikin masu zuba jarin akwai wanda ya kafa Flutterwave, Olugbenga Agboola, da O.O. Nwoye da Abdulhamid Hassan na Mono, da Nathan Nwachukwu na Terra Industries.
Sabon jarin na iya ɗaga darajar kamfanin zuwa tsakanin dala miliyan 15 da dala miliyan 30. Lagos Life wasa ne da ke ba mutane damar ƙirƙirar hoton kansu na zamani, samun ayyukan yi, hulɗa da wasu, sayayya da mallakar gidaje ko filaye a birnin intanet.
Wasan ya fara ne da birnin Ikoyi na Legas, inda ya samu rajistar masu amfani miliyan 1 cikin kwanaki 3 kacal.
Kamfanin na shirin faɗaɗa shi zuwa Abuja da Fatakwal. Ya kuma fara samun kuɗaɗen shiga ta tallace-tallace da tallata waƙoƙin mawaka, inda kuɗin shigarsa suka haura dala 170,000.
Shalom Rayhamen, wadda ta kafa kamfanin, ta ƙirƙiri wasan cikin dare guda ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Nasarar Lagos Life na nuna yadda 'yan ƙirƙira a Afirka za su iya amfani da fasahar AI wajen gina wasanni da sabbin hanyoyin kasuwanci a intanet.
Yarjejeniyar da Hukumar Kare Bayanai ta Ƙasa (NDPC) ta yi da kamfanin Meta ta jawo tambayoyi kan yadda ake tabbatar da bin dokokin kare bayanan sirri a Nijeriya, musamman bayan rahoton tara kamfanin $32.8 miliyan kan zargin karya dokokin bayanai.
A watan Oktoba 2025, Meta da hukumar sun cimma yarjejeniya, wadda kotu ta amince da ita a watan Nuwamba.
Yarjejeniyar ta soke tarar, yayin da Meta ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin wasu wajibai na bin dokokin ƙasar, ba tare da amincewa da aikata laifi ba.
A shekarar 2026, Meta ta ƙara shiga shirye-shiryen haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati, ciki har da ƙaddamar da GovGuide Nigeria da shirin wayar da kai kan kare bayanai tare da NDPC.
Wannan ya sake tayar da tambayar yadda haɗin gwiwar gwamnati da kamfanonin fasaha zai shafi aikin sa ido da tabbatar da doka.
A gefe guda, kamfanonin fasahar kuɗi na cikin gida suna fuskantar wa'adin Babban Bankin Nijeriya na Janairu 2027 kan adana da sarrafa bayanan mu'amalar biyan kuɗi a cikin ƙasar. Bin waɗannan ƙa'idoji na iya buƙatar ƙarin kuɗi da sauye-sauye a tsarin fasaharsu.
Muhimmin batu shi ne tabbatar da cewa ana amfani da ƙa'idojin kare bayanai cikin adalci ga duk kamfanoni, na cikin gida da na ƙasashen waje.
'Yan Nijeriya ma suna buƙatar ƙarin bayani kan abin da yarjejeniyar Meta ta ƙunsa da matakan da ake ɗauka don kare bayanan sirrinsu.
Kamfanin Meta ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 10 a Amurka da Kanada sun riga sun kafa nasu mataimakin basirar wucin gadi na Muse AI cikin watanni 1.5 kacal da fara amfani da shi.
Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg, ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton kuɗin shiga na Meta, inda ya ce Muse na samun karɓuwa cikin sauri, har ya kai matsayin manhajar da ta fi kowace manhaja a App Store a kusan kowace rana. Ya kuma ce kusan kashi 25% na mutanen da suka kafa Muse suna amfani da shi a kowace rana.
Zuckerberg ya ce mafi yawan masu amfani da Muse suna amfani da shi ne wajen siyayya ta intanet, inda sama da kashi ɗaya bisa huɗu na masu amfani da manhajar ke yin hakan. Ya ƙara da cewa matsakaicin kuɗin sayen kaya ta hanyar manhajar ya haura dala $200.
Meta na shirin mayar da Muse wani mataimaki na zamani da zai taimaka wa mutane gudanar da ayyukansu, amfani da imel da kalanda, siyayya, adana lokaci da kuɗi, har ma da gina kasuwanci.
Kamfanin ya ce zai samar da manhajar kyauta ga mafi yawan masu amfani, sannan ya samu kuɗin shiga ta hanyar cajin wasu kasuwanci kan cinikayyar da Muse ya taimaka wajen gudanarwa. Haka kuma, masu buƙatar ƙarin fasaloli za su iya biyan kuɗin rajista.
Zuckerberg ya ce Meta na sa ran inganta ƙarfin sarrafa bayanan Muse domin rage kuɗin gudanar da shi da fiye da ninki 10 cikin shekara guda, yayin da kamfanin ke shirin faɗaɗa amfani da fasahar ga biliyoyin mutane a nan gaba.
Bayan shafe shekaru 5 yana jagorantar @AltSchoolAfrica, @AdewaleYusuf_ ya sauka daga matsayin shugaban gudanarwar kamfanin, inda zai ci gaba da kasancewa mamba a kwamitin gudanarwa. Abokin kafa kamfanin, @hackSultan , ne zai maye gurbinsa.
Yusuf ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga buƙatar samun ƙarin lokaci da nutsuwa wajen kula da rayuwarsa da iyalansa, bayan shafe shekaru yana tafiye-tafiye tsakanin Amurka da Afirka.
A ƙarƙashin jagorancinsa, AltSchool Africa ta bunƙasa daga cibiyar koyar da fasahar zamani zuwa babbar makarantar horas da ƙwararru, inda ta horar da ɗalibai sama da 100,000 daga ƙasashe 75 na duniya.
Sabon shugaban, Akintunde, na shirin faɗaɗa ayyukan makarantar ta hanyar ba ɗalibai damar samun takardar shaidar Diploma, sannan su ci gaba da karatun digiri a jami'o'in da ke haɗin gwiwa da AltSchool. Manufar ita ce sauƙaƙa samun ilimin jami'a mai inganci a farashi mai rahusa.
Wannan sauyi na iya buɗe sabon babi ga AltSchool Africa, daga koyar da sana'o'in fasaha zuwa samar da hanyoyin samun shaidar digiri ga ɗaliban Afirka. Amma lokaci ne zai nuna yadda sabon tsarin zai sauƙaƙa musu samun ilimin jami'a.
Tech Hausa retweeted
In less than 24 hours, a single post on our Facebook page reached 1.2 million people
Millions of Hausa speakers remain an untapped audience for many brands.
Want to reach new customers in a language they understand? @TechHausa is your bridge to that audience.
Let's collaborate
Wani sabon rahoton kamfanin PaidHR ya fitar ya nuna cewa ma’aikata 46 cikin 100 a Najeriya suna samun albashin da bai kai ₦200,000 a wata ba. Binciken ya ƙunshi ma’aikata sama da 25,000 daga kamfanoni da ma’aikatu sama da 400, bisa bayanan da aka tattara har zuwa Yuli 2026.
Rahoton ya nuna cewa ma’aikaci na tsakiya a Najeriya yana samun ₦217,000 kafin cire haraji da kuɗin fansho, yayin da kusan ma’aikata 10 cikin 100 ke samun ƙasa da ₦70,000 a wata. Haka kuma, ma’aikata 10 cikin 100 ne kawai ke samun albashin ₦1m ko sama da haka a kowane wata.
Binciken ya kuma bayyana cewa albashi ya bambanta sosai bisa fannin aiki. Ma’aikatan fasaha da AI suna samun matsakaicin albashin ₦418,916, yayin da na kasuwanci da baƙuncin baƙi ke samun kusan ₦80,000. A bangaren jinsi kuma, mata suna samun matsakaicin albashin ₦192,789, idan aka kwatanta da ₦238,103 na maza.
Rahoton ya gano cewa karin albashi yakan fi yawa a shekarun farko na fara aiki, amma bayan shekaru 5, samun karin albashi mai tsoka yana ƙara wahala. Wannan na iya sa ma’aikacin da ya daɗe a kamfani ya riƙa samun ƙasa da sabon ma’aikaci da aka ɗauka bisa sabon farashin kasuwa.
Duk da hasashen cewa matsakaicin albashi na iya kaiwa ₦380,000 nan da 2030 idan ana samun karin albashi na 15% a kowace shekara, rahoton ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin abinci, sufuri da gidaje na iya rage ƙarfin sayen ma’aikata. Wannan na nuna cewa samun albashi mai yawa ba lallai ya nufin ingantuwar rayuwa ba ne idan kuɗin ba sa iya biyan buƙatun yau da kullum.
Ta ɓoye ta fito fili, gabanin shirye-shiryen OPay na sayar da hannun jari a Amurka (IPO), inda bayanan kuɗaɗe suka nuna cewa kamfanin ya tafka mummunar asara ta sama da Naira biliyan 150 ($118.36 miliyan) saboda taurin kan masu cin bashi a Najeriya.
Manhajojin ba da bashi na kamfanin kamar su EaseMoni sun fada tarkon ’yan Najeriya bayan sun rarraba jimillar bashi na dalar Amurka miliyan $927.6 (kimanin ₦tiriliyan 1.28), sai dai kuma kwatankwacin dala $1.28 a cikin kowace dala $10 da aka bayar rance ta kafe, lamarin da ya tilasta wa OPay lashe amansa ta hanyar goge kuɗaɗen a matsayin asarar bashi (Expected Credit Loss).
Ko da yake kamfanin yana ƙoƙarin rufe fuskarsa da cewa ya sami dalar Amurka miliyan $236.12 ta hanyar tsauraran ruwa da tsinallen tara (interest and penalties), wannan gagarumar badakalar rashin biyan bashi ta girgiza harkar ba da lamuni ta intanet a ƙasar.
Shin kana Daga cikin masu cin bashin Opay? Ka biya naka ko kaima ka cikin wadanda suka riƙe masu kuɗi?
Sterling Bank da cibiyar tallafawa sana’o’i ta Cascador sun haɗa gwiwa domin ƙaddamar da wani babban asusun tallafin bashi na dalar Amurka miliyan 200 domin taimakawa ƙananan sana’o’i da matsakaita a Najeriya wajen samun lakadan bashin gudanar da sana’o’insu.
Wannan sabon shiri yana da nufin raba kasadar bashi tsakanin asusun da cibiyoyin ba da bashi, wanda hakan zai bawa bankuna kwarin gwiwar fitar da babban bashi na dogon lokaci.
Cascador ta bayyana cewa wannan tsari yana da damar fadada ikon bayar da bashi har zuwa dalar Amurka biliyan guda a tsawon lokaci.
Gidajen sana’o’in da wannan shiri ya sa gaba sune waɗanda suka riga suka nuna ƙarfin tafiyar da bashi amma suke fuskantar ƙalubalen samun nasara wajen ciro kuɗaɗen daga bankuna.
A matakin farko, kasuwancin da suka dace za su iya samun bashin kuɗin gida da ya yi daidai da dalar Amurka dubu 250, tare da burin buɗe ƙofar samun bashin da ya kai dalar Amurka miliyan guda da zarar asusun ya cika gaba ɗaya.
Shugabar gudanarwa ta Cascador, Trish Thomas, ta bayyana cewa ta hanyar raba kasada tsakanin masu ba da bashi da kuma amfani da amincin al’umma a matsayin wata shaida mai ƙarfi ga bankuna, asusun zai taimaki kasuwanni da dama wajen samun abin da suke buƙata domin faɗada kasuwancinsu da kuma samar da abun yi ga mutane.
Ana saɓon gina tushen kuɗaɗen wannan asusu ne daga agajin ƙungiyoyin sa-kai, masu zuba jari domin rage radadin al’umma, da kuma cibiyoyin kuɗi na ci gaba. Wannan mataki ya biyo bayan fitar da wata takardar nazari ta Cascador mai taken The Multiplier Model, wacce ta nuna cewa kashi 22 kacal na sana’o’i a yankin kudu da hamadar Sahara ne ke da asusun bashi na banki, wanda ya yi ƙasa sosai da matsakaicin adadin duniya na kashi 36.
Obinna Ukachukwu, wanda yake gudanarwa a bankin Sterling Bank, ya bayyana cewa wannan tsari zai haɗa kasuwancin da aka ba da shawararsu daga cibiyoyin zuba jari da ke da cikakken saninsu. A cewarsa, wannan tsari zai kawo masu cin bashi ingantattu gami da sauƙaƙe duba ƙarfin kasuwancinsu da ci gaba da sa ido a kansu, wanda ke ba banki kwarin gwiwar ba su babban bashi na lokaci mai tsawo.
Za a tafiyar da wannan asusu ne ta hanyar kamfanin Riverwell Platform Holding Limited wanda yake mallakar ƙasar Birtaniya gami da reshensa na Riverwell Platform Services Nigeria. Shi kansa asusun ajiyar za a riƙe shi a keɓe, kuma Obinna Ukachukwu zai kasance ɗaya daga cikin daraktocin dandalin na Riverwell.
Wannan sabon tsari ya ginu ne a kan gwajin da Cascador da Sterling Bank suka yi a baya. Cascador ta bayyana cewa tun daga shekara ta 2019 ta samun nasarar tallafawa kasuwanni 80 wanda hakan ya taimaka musu wajen tara kuɗaɗen zuba jari da suka wuce dalar Amurka miliyan 150.
Kamfanin Apple ya kaddamar da wata sabuwar na'ura mai kwakwalwa ta gida mai suna 'Apple HomeView' akan farashin $299 (₦403,650).
Wannan na'ura, wadda take da babban dan ƙaramin allo mai girman inci 7, tana amfani da sabon tsarin fasahar zamani na Siri AI da kuma gajeren sassa na A18 chip domin tafiyar da al'amuran gida cikin sauki.
Za a fara sayar da ita a hukumance ranar 13 ga watan Nuwamba, 2026.
Abubuwan da na'urar ta kunsa sun hada da:
Na'urar na iya gane fuskokin mutane har su shida a gida guda, inda take canza abubuwan da ke kan allo domin nuna sako da jadawalin kowane mutum daban.
Manhajar Siri da take iiya amfani da bayanan mai amfani da ita domin gudanar da ayyuka a cikin manhajoji daban-daban cikin sauri.
Allon na'urar yana kulfe kansa kai tsaye idan wani bako ko wanda ba a sani ba yayi yunkurin leken asirin mai na'urar.
Tana iya nuna hoton kyamarori tara na gida a lokaci guda, kuma tana aiki tare da sabbin kayayyakin gida na kamfanonin LG da Schneider Electric.
’Yan Najeriya Sun Yi Amfani da Intanet Har Terabytes Miliyan 11.94 Cikin Watanni 8 na 2026 techhausa.com/yan-najeriya-s…
Kamfanin Sadarwa na Glo Ya Rasa Abokan Ciniki Kusan Dubu 46 a Watan Agusta 2026 techhausa.com/kamfanin-sadar…
Wata babbar sanarwa mai firgitarwa ta gidauniyar fasaha a kasar Kenya da ma shiyyar Afirka baki daya ta fito fili bayan da kamfanin Microsoft ya sanar da ma'aikatansa cewa yana shirin rufe cibiyarsa ta Africa Development Centre wato ADC da ke birnin Nairobi a ƙasar Kenya
Wannan mataki da aka bayyana wa ma'aikatan a ranar Litinin 12 ga watan Oktoba na shekarar 2026 yana zuwa ne a matsayin wani bangare na sauye-sauyen da kamfanin ke yi a matakin kasa da kasa domin sake tsara fasalin gudanar da ayyukansa.
Cikin daftarin labarin da ake samu daga cikin ma'aikatan sun nuna cewa al'amarin ya girgiza bangaren fasaha na kasar Kenya sosai domin cibiyar ta kasance daya daga cikin manyan ginshiƙan bunkasa hazakar matasa a fannin da sarrafa na'ura mai kwakwalwa da tsara aikace-aikace.
Duk da cewa kamfanin Microsoft bai fito fili ya bayyana adadin ma'aikatan da wannan rufe bangaren zai shafa ba a halin yanzu cibiyar da ke gini mai suna Dunhill Towers a yankin Westlands na birnin Nairobi tana dauke da tsakanin kwararrun ma'aikatan fasaha 450 zuwa 570.
Kamfanin ya fayyace cewa wadannan sauye-sauye da ake shirin yi sun shafi sashen injiniyanci kawai yayin da sauran ayyukansa na kasuwanci da kuma tallata hajoji gami da ba abokan ciniki goyon baya za su ci gaba da gudana a kasar Kenya ba tare da wata tsaiko ba.
Sakamakon wannan labari sakataren ma'aikatar watsa labarai da fasahar sadarwa ta kasar Kenya William Kabogo ya gudanar da wani taro na gaggawa da manyan shugabannin kamfanin Microsoft domin tattaunawa kan hanyoyin kiyaye basira da gwaninta ta ma'aikatan cikin gida na kasar Kenya gami da kare ayyukan su.
Bangarorin biyu a halin yanzu suna gudanar da aiki tare domin fito da wani tsari guda wanda zai maida hankali sosai kan bunkasa amfani da fasahar basira ta AI da mayar da ayyuka tsarin na'ura mai kwakwalwa da kuma karfafa tsaro a yanar gizo.
OPay Na Shirin Shiga Kasuwar Hannayen Jari ta Amurka, Kimarsa Ta Kai $4 Biliyan techhausa.com/opay-na-shirin…
NCC Ta Fara Katse Hanyoyin Sadarwar Wasu Wayoyin Najeriya: Ga Yadda Za Ka Kare Wayarka techhausa.com/ncc-ta-fara-ka…
Bayani game da taron FasaHer da za a gudanar a Kano daga bakin Safiyya Daba.
Za a gudanar da taron ne a Baba Ahmad University, Sharada, Kano.
Ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026.
#FasaHer2026 #ItaDaFasaharTa #HerTechHub #ArewaWomenInTech #HausaTech #WomenInTech #NorthernInnovation #KanoTech
Wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙin amfani da intanet, wato Foundation for Digital Justice and Sustainable Development, ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda take ƙalubalantar abin da ta bayyana a matsayin haramta ko taƙaita amfani da manhajar TikTok a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
A cikin takardar ƙarar, ƙungiyar ta zargi kamfanin na TikTok da amfani da dabarar geoblocking wato tauye wa masu yankuna amfani damar shiga manhajar ko amfani da ita a jihohin Kano, Kaduna, Kebbi, da kuma Sokoto.
Batutuwan da Ƙarar Ta Kunsa
Ta hannun lauyanta, Festus Ogun, ƙungiyar ta buƙaci kotu ta tuhumi Tiktok tare da ba da gaskiya a kan batutuwa kamar haka:
1. Yancin Faɗar Albarkacin Baki: Shin matakin taƙaita shiga manhajar ya saɓa wa haƙƙin ƴan ƙasa na faɗar albarkacin baki da tsarin mulki ya ba su?
2. Nuna Bambanci: Shin haramtawa ko takurawa mutanen wani yanki na musamman na ƙasar nan ba ya nuna bambanci tsakanin masu amfani da manhajar a sassan Najeriya?
Abubuwan da Ƙungiyar ke Buƙata Daga Kotu
Ƙungiyar ta roƙi kotun da ta yanke hukunci akan hukunan da suka haɗa da:
Bayyana Haramcin Matakin, wato Ta bayyana cewa matakin taƙaitawar bai dace da doka ba kuma ya saɓa wa tsarin dokar kasa.
Cire Takunkumi Nan Take, Kotun ta ba TikTok umarnin ta cire dukkan wasu takunkumi da ta sanya, tare da hana ta sake aiwatar da irin wannan mataki a Arewacin Najeriya ba tare da ingantaccen dalili na doka ba.
Daga ƙarshe, Ta buƙaci TikTok ta ba da haƙuri a hukumance a cikin manyan jaridu uku na ƙasa saboda zargin take haƙƙin masu amfani da ita.
Tushen Ƙarar da Matakin Kotu
An shigar da wannan ƙara ne a ranar 5 ga Oktoba, 2026, inda karar ta dogara da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara) da kuma Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙin Bil Adama da na Jama'a.
Haka zalika, kotun ta bayar da umarnin cewa TikTok ta bayyana a gabanta a cikin kwanaki biyar da karɓar sammacin ƙarar, idan ba haka ba, kotun za ta ɗauki matakin da ya dace a kan kamfanin.
Wata ’yar Najeriya mai suna Shalom Mathew ta samu gagarumar nasara bayan wasan da ta kirkira mai suna Lagos Life ya samu sama da masu amfani miliyan daya cikin kwanaki uku kacal.
Shalom, wadda ke aikin software development, ta fara gina wasan ne bayan ta ga wani wasan da aka kirkira kan rayuwar Lagos. Ta yi tunanin kirkirar nata wasan da zai ba mutane damar rayuwa a cikin Lagos.
Abin mamaki shi ne, ta samu nasarar gina wasan cikin kasa da awanni 12, inda ta yi amfani da kwarewarta da kuma AI wajen taimaka mata wajen rubuta da gyara wasu sassan code.
A cikin wasan, mutum zai iya kirkirar halinsa, samun aiki, samun kudi, biyan haya, sayen gida da kuma yin abubuwan da suka yi kama da rayuwar yau da kullum a Lagos.
Bayan kaddamar da shi, wasan ya fara yaduwa sosai a shafukan sada zumunta, inda cikin kwanaki uku kacal ya samu sama da masu amfani miliyan daya.
Daga baya kuma Shalom ta fara samun kudin shiga ta hanyar tallace-tallace da kamfanoni ke sanyawa a cikin duniyar wasan.
Idan ka taɓa ƙoƙarin karɓar wani kaya da aka kawo maka ta hanyar mota ko babur a Najeriya, babu shakka ka san yadda kwatancen adireshi ke zama doguwar rigima. Wani lokaci takan kai ga ana ɗaukar mintuna 20 ana waya da mai kawo saƙon domin ya gano inda kake.
Amma yanzu, gwamnatin tarayya ta fito da wata sabuwar dabara don kawo ƙarshen wannan matsala ta hanyar gabatar da sabon tsarin lamba na zamani wanda zai sauƙaƙe gano kowane gida da ke faɗin ƙasar.
Wannan sabon tsirin da ake kira National Digital Alphanumeric Postcode System yana maye gurbin tsofaffin lambobin gida guda shida na kamfanin NIPOST da wasu sabbin lambobi da haruffa guda goma sha ɗaya. Wannan sabuwar dabara tana da ikon nuna takamaiman ginin da ake nema ba tare da ɓata lokaci ba.
Maimakon lamba guda ɗaya ta shafi unguwa guda ɗaya da ake amfani a baya, sabon tsarin yana rarraba wuri ne daga matakin jiha zuwa ƙaramar hukuma, unguwa, yanki, har zuwa ga takamaiman ginin da mutum yake.
Misali mai sauƙi na iya zama kamar FD 05 B04 KB 07, wanda hakan zai sauƙaƙe gano wurin ba tare da dogon bincike ba. Wannan tsari yana samuwa ne ta hanyar manhajar sadarwa ta zamani ta NIPOST. Idan har ba a tsara ginin ku a cikin tsarin ba tukuna, za ku iya tura lambobin wurin naku na GPS ko kuma ta hanyar amfani da Google Maps domin a tantance shi tare da saka shi a cikin littafin adireshi na ƙasar.
Wannan sabon cigaba yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar yau da kullum ta ‘yan Najeriya. Ka yi tunanin dukkan abubuwan da suka dogara da sanin inda wani yake a zahiri, kamar kawo abinci gida, cinikin yanar gizo, jigilar fasinjoji, agajin gaggawa, da kuma bankunan da ke buƙatar tabbatar da wurin da abokan cinikinsu suke zaune.
Samun ingantaccen adireshi na zamani zai rage kiran waya na tambayar alamun gida, ya rage asarar kayayyaki, kuma ya ba ‘yan kasuwa damar isa ga abokan cinikinsu cikin sauƙi ko da suna nesa.
Gwamnati tana da burin ganin wannan tsari ya zama wani babban jigo a cikin harkokin fasaha na Najeriya. Akwai kuma shirye-shiryen haɗa shi da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi domin sauƙaƙe ayyuka. Duk da yake wannan wani babban cigaba ne mai kyau, har yanzu akwai manyan tambayoyi kan yadda jama'a da kamfanoni za su karɓe shi hannu biyu-biyu.
Kamfanin NIPOST ya buɗe ƙofofinsa ga masu ƙirƙirar manhajoji da ‘yan kasuwa domin amfani da tsarin. Sai dai samun cikakken dama ga bayanan wurare yana buƙatar tantancewa daga kamfanoni da kuma biyan kuɗi ta hanyar amfani da kiredit, yayin da takamaiman lambobin wuri ke fuskantar wasu taƙaitawa.
Wannan shi ne zai ƙayyade yadda da sauri ‘yan kasuwa da sabbin kamfanoni masu tasowa za su haɗa sabon tsarin lambar gidan a cikin harkokinsu na yau da kullum.
Gaskiyar magana ita ce, ƙirƙirar tsarin adireshi na fasaha abu ne guda, amma samun kowa da kowa, tun daga hukumomin gwamnati zuwa manhajojin jigilar kaya da ƙananan ‘yan kasuwa, su amince su yi amfani da shi abu ne daban da ke buƙatar haɗin kai da kuma wayar da kan jama'a sosai.
Shin kana ganin wannan sabon tsari zai kawo sauƙi a harkokin yau da kullum na masu kawo kaya da sufuri a yankinku?















